Wannan shi ne hari na uku a jere da kungiyar ke kai wa cikin wannan watan a birnin, galibi kan mabiyan darikar Shi’a.
Harin ya auku ne, a dai-dai lokacin da dubban al’umma ke gudanar da bikin cika shekaru 38 da mamayar da tarayyar Soveit ta yi wa Afghanistan a wata cibiyar al’adu a yammacin birnin, inda nan ne ake da wata ofishin wata jarida mai yaki da ayyukan ta’addancin kungiyar IS da ake kira Afghan Voice Agency.
Mai Magana da yawun ma’aikatar lafiya na Afghanistan Waheed Majroh ya shaidawa manema labarai cewa kawo yanzu akwai gawar mutane sama da 50 yayinda kuma wasu 84 ke karbar kulawar gaggawa.
Wani ma’aikaci a kafar yada labaran wanda ke wurin lokacin da aka kai harin, ya ce cikin wadanda harin ya rutsa da su akwai da dama daga cikin ma’aikatansu.